26 Satumba 2020 - 15:44
Abbas Ya Bukaci Taron Kasa Da Kasa Kan Rikicin Falasdinu Da Isra’ila

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya bukaci wani taron kasa da kasa a farkon shekara 2021 mai zuwa kan rikicin Falasdinu da Isra’ila.

ABNA24 : A jawabinsa na babban taron zauren MDD, Mahmoud Abbas, ya yi fatan taron zai samu goyan bayan da ake bukata domin samar da shirin zaman lafiya na gaskiya domin kawo karshen mamayar Isra’ila.

Haka zalika Mahmood Abbas, ya soki matakin wasu kasashen larabawa na baya baya nan musamman Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Bahrein na kulla alaka da Isra’ila a karkashin jagorancin Amurka.

342/